Canje Canjen Mulki a Arewa Bayan Rasuwar Sardauna

Canje Canjen Mulki a Arewa Bayan Rasuwar Sardauna

 



A ranar ta 15 ga janairu 1966 kwamandan sojojin nigeria manjo janar Aguiyi Ifenyi Chukwu Ironsi ya karbi ragamar mulkin nigeria, kuma ya gabatar da dokar soja ta dakatar da ofishin shugaban kasa (President), wazirin kasa (Prime Minister), da majalissar tarayya (Parliament).

An gabatar da wata dokar dai data rushe ofishin gwamnonin jahohi (Regional Governors), firimiyoyin jahohi (Regional Priemiers), da majalissar jahohi (Regional Parliament),  haka dai an rushe dukkan majalisun zartarwa na tarayya da jihohi (Federal and Regional Executive Concil).

An kafa dokar gwamnatin mulkin soja a dukkan jihohi wanda suke karkashin gwamnatin mulkin soja ta tarayya (FederalMilitary Government FMG).

A kaduna kuwa dan ta'adda manjo Nzeogwu ya sanar da kafa gwamnatin ma'aika domin Arewa, wadda zata kawar da kabilanci, son kai, da akidar yanki - yanki (Regionalism).

Wadanda Ironsi ya nada sun hada da manya ma'aikan arewa da ke kaduna kamar haka,

1. Ali Akilu
2. Ahmed Talib
3. I.J.D Durlong
4. Barlow Pole
5. Ahmed Joda
6. Muhd Lawan
7. Muhd Gujbawu
8. Bukar Shu'aib
9. Yusufu Gobir
10. A.C Mackeller
11. Ibrahim Dasuki
12. E. Jones.
13. J.W. Barley
14. S. Ade John
15. Dr. R.A.I Dikko
16. Ibrahim Argung
17.Abdullahi Kure
18. Liman Ciroma

Post a Comment

Previous Post Next Post