An Gurfanar Da Matashin Da Yake Sace Kofofi Da Rufin Masallatai A Kotu - Jigawa

An Gurfanar Da Matashin Da Yake Sace Kofofi Da Rufin Masallatai A Kotu - Jigawa


A ranar Alhamis din data gabata ne a ka gurfanar da Abba Haruna, dan shekara 21 da ke damfarar masallatai, sai ya yaye rufi da kuma cire kofofin masallaci ya gudu da su ya sayar.

Tun da fari, dubun Haruna ta cika ne bayan ya yaudari mutanen kauyen Konake a garin
Kiyawa, Jihar Jigawa cewa larabawa ne su ka bashi kwangilar gyara babban masallacin kauyen.

Da ga bisani ne ya sanya a ka cire rufin
kwanon masallacin da kuma kofofin, inda ya ranta a na kare, sai dai kuma tuni dubunsa ta cika bayan da jami'an tsaro su ka kafa masa tarko, su ka kuma samu nasarar cafke shi a Jigawa.

Wakilin mai unguwar Konake, Ussaini
Wanzam Ilyasu, ya ce mako biyu da suka
gabata ne matashin ya je garin nasu, ind ya
ce wata kungiya daga kasar Larabawa za ta
gina musu sabon masallaci, saboda haka za
a rushe tsohon.

Tuni dai a ka gurfanar da mai laifin a kotun Majistare ta gurfanar da shi a yau a Jigawa, inda mai gabatar da kara ya ce a na zargin shi da zamba, sata da almundahana.

Bayan an rushe wani É“angare na masallacin
sai ya ce ciko za a yi da shi, sannan ya zuba
kofofi da tagogi da kwano da famfon tuka-
tuka a mota suka tafi da su," a cewar wakilin mai unguwa.

Ya kara da cewa matashin ne da kansa ya
biya ma'aikatan da suka yi aikin rushe
masallacin. "Masu cire kwano aka ba su
5,000, su ma masu cire wayarin aka ba su
2,000. Masu bige haraba ma anba su 5,000


Reported by: Abubakar D. Bature

Post a Comment

Previous Post Next Post