Wahalar Fetur Ta Sa An Mayar Da Hutun Mako Kwana 3 A Sri Lanka

Wahalar Fetur Ta Sa An Mayar Da Hutun Mako Kwana 3 A Sri Lanka


 

Gwamnatin Sri Lanka ta amince da karin kwanakin hutun karshen mako zuwa kwana uku har zuwa tsawon wata uku masu zuwa ga galibin ma’aikata, sakamakon matsalar karancin man fetur wanda kasar ke fuskanta a halinn yanzu.

Tun baya da aka fara rikicin rasha da ukraine aka Fara samun karancin man fetur, iskar gas,  Alkama, da sauran kayan masarufi. Sri Lanka ta shiga fatara a asusun ajiyar kudadenta na waje kuma karancin shigo da mai ya haifar da wahalar mai a cikin kasar.

Wani babban Ministan kasar ya ce ranar Juma’a za ta kasance ranar hutu ga yawancin ma’aikatan da ke aiki a ma’aikatun da ba na bukatu ta musamman ba, Tsarin ba zai shafi ma’aikata a muhimman sassa kamar bangaren kiwon lafiya da makamashi da ilimi da kuma tsaro ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post