Kungiyar Masu kula da Kungiyoyin Kwallon kafa ta Kasa ta dakatar da shugaban kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Yahaya Surajo har sai baba-ta-gani, saboda halin da ya nuna a lokacin wasan mako na 31 da kungiyar ta kara da Dakkada FC a Kano a jiya Alhamis din data gabata A cikin wani faifan bidiyo ne, a ka ga Surajo ya kai wa wani mataimakin alkalin wasa naushi a wasan, lamarin da kungiyar ta bayyana a matsayin abin takaici, wanda ba za ta amince da shi ba kuma hali da zai iya bata mata suna.
Don haka kungiyar masu kula da kungiyoyin kwallon kafa din ta dakatar da shugaban kungiyar ta Kano Pillars, Malam Yahaya Surajo daga dukkan ayyukan kungiyar har zuwa lokacin da za a gudanar da cikakken bincike kan lamarin, a cewar Alloy Chukwuemeka, Sakataren zartarwa na kungiyar.
wannan Kungiya ce da ta hada da hazikan masu kula da kwallon kafa wadanda suka yi fice a Bangarori da dama na fannin rayuwa da ake saran za su ba da horo sosai wajen gudanar da kungiyoyin kwallon kafa daban-daban. Kungiyar ta fusata kan halin Surajo wanda ya zo kasa da sa'o'i 48 bayan wani taron hadin gwiwa da LMC, inda ta yi gargadi game da ayyukan da za su iya haifar da mummunan zato ga gasar. Shugaban kungiyar Barr. Isaac Danladi, yace ciyaman din na Kano Pillars zai fuskanci kwamitin ladabtarwa don kare kansa kafin a sake shigar da shi cikin kungiyar.
SOURCE: Daily Nigerian