A yau Alhamis ne Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da matatar mai ta kamfanin
Duport Midstream Energy Park a unguwar Ogbekor, Karamar Hukumar Orhionmwon a
jihar Edo.
Matatar za ta kasance za a rika tace ganga
10,000 a kowace rana, inda a ke sa ran za ta
fara tace gangar mai 2,500 a ranar da ga ranar 28 ga watan Yuli, da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala rangadin ginin matatar, Simbi Wabote, Babban Sakataren hukumar Bunkasa wa da sa ido a kan kayayyakin da ke samarwa na cikin gida, NCDMB, ya ce matatar ta kasance ta biyu da za a bude a watan Yuli.
READ ALSO: Tinubu Yasha Da Kyar A Jihar Lagos, Inda Wasu Fusatattun Matasan Yarbawa Suka Kai Masa Hari
• Gwamnan Legas ya Raba Sabbin Motoci 13 ga Gwarazan Malamai - Asua Daily Post
Tsarin shi ne a ranar 18 ga watan Yuli, DPR
za ta zo ta yi bincike na karshe game da ba
mu izinin shigar da iskar gas a cikin matatar. Don haka, daga yanzu zuwa karshen watan Yuli, wannan matatar man ban da wadda muke da ita a Ibigwe, za ta fara aiki.
Game da aikin matatun mai na zamani, nan
da watan Yuli, wannan zai ci gaba da nuna
muku cewa akwai matatun mai da ke aiki a
kasar nan, muna godiya ga abokan huldarmu, NNPC da kuma Seplat da suke samar mana da danyen man da ake so. A nan, muna aiki tukuru tare da kamfanin mai na summit mai da sauran abokan hulďa da ke son hada gwiwa da mu don samar da danyen mai.
A halin yanzu, daya daga cikin matatun man namu ta na aiki, wanda shine Watersmith modular matatar mai da ke tace ganga 5,000 a rana da za ta rika samar da mai ga kasuwar gabashin kasar nan
Reported by: Salisu Muhammad