Ganduje Ya Sayar Da Wani Bangare Dake Makarantar Sakandire Ta Gss Kofar Nassarawa An Fara Gina Shaguna - Asua Daily Post

Ganduje Ya Sayar Da Wani Bangare Dake Makarantar Sakandire Ta Gss Kofar Nassarawa An Fara Gina Shaguna - Asua Daily Post

 



Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Ta Ruguje wani bangare na GSS Kofar Nassarawa, an fara gina shaguna domin su kalli Titin IBB dake Kasuwar kwari, a Jihar Kano, Duk da tabarbarewar ajujuwa da makarantar ke fama da shi sakamakon gazawar gwamnati, dalibai suna daukar karatu a hakan, mai makon gwamnati ta mayar da hankali kan wannan aikin na gyaran ajujuwa amma ta fara sayar da wani bangare tare wasu ajujuwa da aka dena daukar karatu acikinsu na makarantar.

Al'ummar jihar Kano na kokawa kan yadda gwamnatin ke ci gaba da sayar da masallatai,  makarantu, gonaki, kasuwanni da filayen jama'a domin azurta kai.

A kwanakin baya in baku mantaba  gwamnati ta tura jami'an tsaro domin murkushe 'yan kasuwar Rimi ('yan tebura) domin gina shaguna a gurin nasu, ba tare da tunanin halin da masu neman kaiwa nabaka a gurin zasu shiga ba duk da cewar sun kwashe shekaru suna gudanar da kasuwancin su a yankin.

Post a Comment

Previous Post Next Post