Daliban Jihar Kano Kimanin Su Dubu Goma Sha Biyar Bazasu Rubuta Jarabawar NECO Ba Sakamakon Bashin Da Ake Bin Gwamnatin Jihar

Daliban Jihar Kano Kimanin Su Dubu Goma Sha Biyar Bazasu Rubuta Jarabawar NECO Ba Sakamakon Bashin Da Ake Bin Gwamnatin Jihar


Kimanin daliban jihar Kano dubu sha biyar ne ba za su zana jarrabawar kammala sakandare ta shekarar 2022 da Hukumar Jarrabawa ta kasa (NECO) ke gudanarwa saboda bashin Naira Biliyan N1.5billion da hukumar ke bin gwamnatin jihar.

Duk da cewa a ranar Litinin 27 ga watan Yuni, 2022 ne, Hukumar NECO za ta fara Jarrabawar SSCE na 2022.

Majiyoyi sun shaidawa jaridar Solacebase cewa hukumar jarabawar ta sha alwashin cewa daliban Kano ba za su rubuta jarabawar shekarar 2022 ba saboda dimbin bashin da ake bin gwamnatin na kimanin naira biliyan N1.5billion.

READ ALSO: Ganduje Ya Sayar Da Wani Bangare Dake Makarantar Sakandire Ta Gss Kofar Nassarawa An Fara Gina Shaguna - Asua Daily Post

Da take tabbatar da yuwuwar faruwar lamarin a ranar Lahadi, babbar sakatariyar ma’aikatar ilimi ta jihar Kano, Hajiya Lauratu Ado ta Bayyana cewa gwamnatin jihar Kano ta fara tattaunawa da hukumar NECO kan shawo kan lamarin.

Ta ce gwamnatin jihar ta biya NECO naira Miliyan N356m a makon da ya gabata amma hukumar jarabawar ta dage sai an biya naira miliyan N700m kafin a bar daliban jihar su zana jarabawar.

"Mun yi mamakin yadda Hukumar NECO ta ki amincewa da bukatun mu bayan Gwamnatin jihar ta biya hukumar naira Miliyan N356m, kuma ta rubuta wa hukumar takardar alkawari cewa za a cigaba da turo wa hukumar naira miliyan N50m duk wata" in ji babbar sakatariyar Ma'aikata

Post a Comment

Previous Post Next Post