An Yankewa Dan Gudun Hijirar Afghanistan Hukuncin Kisa Tahanyar Rataya Bisa Kisan Malamai 2 a Iran

An Yankewa Dan Gudun Hijirar Afghanistan Hukuncin Kisa Tahanyar Rataya Bisa Kisan Malamai 2 a Iran

 



A ranar litinin din data gabata aka zartar da hukuncin kisa kan wani É—an gudun hijira É—an Æ™asar Afganistan a Iran bisa laifin kisan wasu malaman Shi’a guda biyu a farkon wannan shekarar.

An rataye matashin mai shekaru 21 a gidan yarin Vakilabad da ke arewa maso gabashin birnin Mashhad, kamar yadda shugaban hukumar shari’a ta yankin ya sanar, a cewar kafar yaÉ—a labarai ta Misan.

Rahotanni daga kafafen yaÉ—a labarai na cewa, Al'amarin ya  faru ne a birnin Mashhad da a ke yin ibadar ta musamman a hubbaren Imam Reza na Shi’a.

Akwai kuma wasu masu laifin guda shida. Mutum na uku da aka kashe ya samu munanan raunuka a harin, an ce harin na da alaka da addini.

A cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, akwai kusan ‘yan gudun hijira miliyan biyu da ba su yi rajista ba daga Afghanistan da ke zaune a Iran.

Shi’a Musulunci shi ne addinin gwamnati a Iran. An samu rarrabuwar kawuna tsakanin ‘yan Sunni da ‘yan Shi’a a Musulunci, kuma sau da yawa ana samun sabani a tsakanin su.

Reported by: Abubakar D. Bature

Post a Comment

Previous Post Next Post