Yadda zaku hada Application a Wayarku Ta Android Cikin Sauki

Yadda zaku hada Application a Wayarku Ta Android Cikin Sauki

 


Barkan ku da war haka, Sannan kuma barkan ku da kasancewa a wannan shafi Na "Asua Daily Post" mai albarka, A yau ina so in yi magana ne kan yadda zaku Hada Application naku na kanku a wayarku Ta Android Cikin sauki. Ba tare da ko sisi ba.

Da fari Kuna bukatar Browser mai kyau da zaku yi wannan Aikin dashi, a cikin wannan post Na tattaro Browsers Guda biyu da za su yi wannan Aikin, sai a zabi guda daya ayi downloading nashi idan kuma kuna da shi to shikenan ba bukatar kayi downloading.

• Chrome
• Firefox

Bayan kunyi downloading Browser Sai ku shiga cikin browser din, idan kuka shiga a sama wajen rubuta address sai ku rubuta www.andromo.com sai ku bashi Go ko next, idan ya gama Loading zai kawo ku Website na Andromosai ku danyi scrolling Kasa ku dan tura website din sama, a kasa za kuga Signup Now for free.

ALSO READ: Yadda Ake  Bude Paypal Account Cikin Sauki

Sai ku danna kai zai kawo ku wani page inda zaku yi register.

Da fari akwai Username: wato sunan da zaku yi amfani dashi a site nasu, sai ku zabi suna sai dai idan zaku rubuta sunan ku ya zama da kananan haruffa tun daga farko har karshe misali “adbature” haka ake so ya kasance ba tare da anyi Amfani da manyan Harrufa ba.

To bayan wannan sai Email naku, sai ku rubuta email domin ta email naku ne za’a turo muku application din da kuma sauran muhimman abubuwa, ayi kokari asa email mai kyau idan ba haka ba babu abunda zai yiwu.

To bayan wannan sai password, wato nombar sirri, sai ku saka wanda zaku tuna kar ya kasa nomba ko haruffa takwas(8), sai ku je rukuni na gaba za kuga password confirmation, to anan ana so ne a maimata password da aka sa a sama idan ansa shikenan.

Bayan wannan sai reCaptcha,
Zaku ga I am not a robot sai ku danna gefen da kuka ga alamar box to sai ku jira shi, wani lokaci zakuga yayi confirming ba tare da kun danna komai ba amma yawanci zai nuno muku hutuna yace ku zabi wanda akwai mota, ko keke, ko kogi, ko jirgin kasa ko wani abu makamancin haka.

To a cikin hotunan sai ku zabi wanda kuka ga akwai abinda suka tambaye ku, shikenan idan yayi confirming sai ku danna Create Account, Idan kuka danna create zai nuna muku wata sako a sama kamar haka “a message with a confirmation link has been sent to your email address. Please open the link to activate your account”

RELATED: Yadda Aka Kirkiri Wayar Hannu Aduniya

Ma’ana sun turo muku sako domin kuyi activating na account, sai ku shiga Email naku, za kuga sako daga Andromo sai ku shiga, idan kun bude zakuga sakon toh sai ku duba a hankali za kuga “confirm my account”

Toh idan kuka danna kan confirm my account zai kawo ku browser naku, sai ku barshi yayi loading idan yagama zai nuno muku “your account was successfully confirmed”

Shikenan kun bude account a Andromo a bunda ya rage yanzu sai ku yi Login Kusa email naku da kuka yi amfani da Password naku da kuka sa dazu, sai ku confirming reCAPTCHA irin na dazu shikenan idan kun gama sai ku danna kan Login.

To yanzu kun bude account saura ku fara kirkiran application naku, ku duba zaku ga “create New App” sai kawai ku danna kai.

Idan ya gama Loading zai nuna muku ku  rubuta Sunnan da kuke so ku kirkiri Application din dashi idan kuka sa sunan sai ku danna “Create”

Shikenan sai ku tsara irin application din da kukeso ku kirkira.
Sannan kusani bada iya andromo kawai ake
Kirkirar application ba wasu site din kamar haka:

•appgeyser.
•tunkable.
Da dai sauransu.


Written by: Abubakar D. Bature

1 Comments

Previous Post Next Post