Ayau "Asua Daily Post" tazo muku da hanya mafi sauki da ake hada na,uran kyankyasan kwan kaza wanda akafi sani dasuna incubator wanda yake amfani da wutan lantarki. Daga farko mai karatu ya karanta bayanin anitse domin yafahimci yadda bayanin yake.
1. Daga farko anaso kasami gidan da
zaka hada na na,uran, idan kaga dama zaka sami empty na kwalin Tv ko kwalin karamin fridge ko kuma wani gidan katako idan zaka iya hadawa saika hada gidan katakon yayi kama da tsarin square box.
2. Ana so kasami kwan wutar lantarki ko fitilar kwai mai amfani da kalanzir (kerosine) kasa aciki, amma karkayi amfanida irin farin kwan wutan lantarki, Kasayi normal jan kwai 60 watt.
3. Bayan kasa kwai wuta kamar yadda
Muka fadama a baya to saika zuba kwan kazarka ka aciki, yadanganta da yawan koyin idan space din dake cikin sa zai dauki kwai goma ko 8 to saikasa, amma kada kasa kwayayen kajin da yawa a ciki.
KALLI VIDEO YADDA AKE HADAWA 👇
4. Kanemo dan karamin kofi ko kwano saika zuba ruwa saika saka kwanon ruwan acikin incubator dinka, kasata a gefen wajen da kazuba kwaikwayen kajin.
5. Daga karshe, anaso kullum da safe kajujjuya koyin, da ranama haka, da daddare ma haka, zuwa na tsawon kwana 18 to daga lokacin kadena juyawa, yana cika kwana 21 kajira kaga ikon Allah, domin insha Allahu zasu kyankyashe.
6 Kasayi digital thermometer Akasuwa amfanin sa yana nuna yanayin tempreture din ne, to saika saka thermometer dinka, ba,aso zafin cikin incubator din yayi kasada 97, karkuma yahaura 101, duk dakansa thermometer din zai nuna maka yanada dan karamin screen haka.
Written by: Abubakar D. Bature