Rahotanni sun bayyana cewa dan wasan gaba na Super Eagles, Victor Osimhen ya amince ya koma kungiyar mafi arziki a duniya wato Newcastle United An ce dan wasan na Najeriyar ya amince ya koma club din gasar Premier ta Ingila a kan kudi kusan Yuro miliyan 4.5 (kimanin N3.4billion).
Dan wasan na Napoli zai iya taka leda a gasar Premier ta Ingila a kakar wasa mai zuwa bayan rahotanni sun ce ya amince da yarjejeniyar sirri da Newcastle United.
Dan wasan na Najeriya na daya daga cikin 'yan wasan gaba da ake nema ruwa a jallo sakamakon rawar da ya taka a kungiyar Napoli ta Serie A a bana,
Rahotanni sun bayyana cewa matashin ya amince da yarjejeniyar da ta kai Yuro miliyan 4.5 da kulob din na Ingila, yayin da Napoli ke ci gaba da tattaunawa da Magpies.
Jaridar The Nation ta ruwaito kamar yadda jaridar La Gazzetta dello Sport ta Italiya ta ruwaito cewa Osimhen ya amince da yarjejeniyar sirri da Magpies a lokacin kasuwar musayar 'yan wasa. Idan yarjejeniyar ta ci tura, dan wasan mai shekaru 23 zai kara tabbatar da matsayinsa na dan wasan Najeriya mafi samun kudin shiga a fagen kwallon kafa a Turai.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa Newcastle na ci gaba da tattaunawa da Napoli ta Italiya kan batun cinikin dan wasan wanda aka ce ya kai kusan Yuro miliyan 100.
Rahoton ya kara da cewa Napoli na neman Yuro miliyan 100 domin kashi 30% na duk wani alkaluman da aka samu kan cinikin Osimhen zai tafi tsohuwar kungiyarsa ta Lille.
Ku tuna cewa La Gazzetta dello Sport ta ruwaito a watan Afrilu cewa dan wasan a shirye yake ya koma Arsenal, amma idan har ta samu gurbin shiga gasar zakarun Turai. Duk da haka, kungiyar ta Premier yanzu maki biyu ne a bayan Antonio Conte na Tottenham a matsayi na hudu da wasa daya kacal.