Barkan ku da kasancewa a wannan shafi namu mai albarka na "Asua Daily Post" a yau ma mun kawo muku kayataccen shirin na mai farin jini na UKU SAU UKU wanda ke zuwa muku daga Tashar, Aka Amfara Youtube Channel.
To in baku manta ba a satin daya gabata an tsaya ne a wurin da aka kama habu wicked, inda bayan An kama shi an kawo shi police station, shigarsa Cell, ke da wuya bayan yagama tumurmusa Sarkin dakin cell din.
Juyowar sa ce da wuya suka hada ido faisal,
Faruwar haka ke da wuya suka kame suma kallon kallo. Inda anan ne aka tsaya shirin satin da ya gabata.
To labari yasha bam, bam inda a shirin wannan Satin habu wicked yake tambayar faisal yagaya masa abinda ya kawo shi police station, Faisal yace tunda kaima bantambaye ka akan me ya kawo ka nan ba ni akan me zaka tambaye ni,
Habu wicked ya fusata yace kai sheda ne ko irin abubuwan da kake gani ina aika tawa basai kayi mamaki ba dan kaganni anan, yace anan nine sarkin daki kuma na tsani ina tambayar mutum yaki bani amsa, kagayamin wane tsautsayine ya kawo ka muka hadu anan.
Faisal yace, wallahi baban budurwa tane yakawo Nan wai yana zargina da sace yarsa, Wicked ya jinjina kai. To banga guda hajiya taji labarin ankama faisalI nda batayi kasa a gwiwa ba ta nufi police station Zuwan ta ke da wuya tashiga in kai tsaye izuwa offis din D.P.O shigar ta keda wuya ta zauna Bayan sun gaisa tace, yallabai wai da gaskene Kun kama faisal, ?
Kudanna wannan link din na kasa ko kuma kudanna bidiyon dake kasan link din domin
Kallon cikakkken shirin kai tsaye.
Uku Sau Uku Season 2 Episode 16
Asha kallo lafiya.
Ok
ReplyDelete