Marigayi Alhaji Abubakar Imam O.B.E, C.O.N, N.N.M.C, (Hon.) an haife shi a garin Kagara dake jihar Niger, da ke Kasar Najeriya a shekara ta 1911. Marigayin ya yi fice wajen rubutun kagaggun labaran Harshen hausa.
Abubakar Imam ya yi karatunsa na boko a jihar Katsina a makarantar nan ta Middle School da ke Katsina da kuma Katsina Training College sannan ya yi karatu a tsangayar ilimi ta jami'ar London da ke Burtaniya.
Bayan da ya kammala karatunsa, ya yi koyarwa a Katsina sannan kuma ya yi aiki matsayin edita na jaridar nan ta Gaskiya Ta Fi Kwabo Sannan ya tallafawa masarautar Katsina ta wancan lokacin karkashin shugabancin Alhaji Muhammadu Dikko inda ya ke fassara rubuce-rubuce daga Larabaci zuwa harshe Hausa.
Alhaji Abubakar Imam ya yi fice ne lokacin da aka sanya wata gasa ta rubutun kagaggun labarai a shekara ta 1933 inda wani littafi da ya rubuta mai suna Ruwan Bagaja ya yi nasara a cikin litattafan da aka rubuta. To bayan wannan littafi, marigayin ya kuma rubuta wasu litattafan da dama da suka hada da "Magana Jarice" da Tarihin Annabi (S.A.W), da Tarihin Musulunci, da tafiya mabudin ilmi, Auren Zobe, da makamantansu.
A cikin 1939, tare da Robert East da wasu tsirarin mutane sun kafa kamfanin Gaskiya, a gidan buga littattafai, wanda ya kaisu ga nasarar ƙirƙirar dandamali ga mutane da yawa, Masanan Arewacin Najeriya.
tsarin siyasa ya sa Imam ya shiga
siyasa a 1952, tare da samuwar Jam'iyyar "Northern People's Congress" (NPC), tare da Umaru Agaie da Nuhu Bamalli, suka kafa manyan tsarikan gudanarwar tsakiya na jam'iyyar.
Marigayi Abubakar Imam na daya daga cikin marubutan da dalibai a matakai daban-daban ke yin nazari kan littafan da suka rubuta da ma nazari akan rayuwarsa,
Allah ya yi masa rasuwa cikin shekara ta 1981 ya kuma bar yara goma sha hudu, maza bakwai da kuma mata bakwai. Muna rokon ubangiji yakai rahama kabarinsa.