Maganin Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Kare Kai Daga Cutar

Maganin Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Kare Kai Daga Cutar


MENENE CUTAR HAWAN JINI:

Ana cewa mutum ya kamu da wannan cuta ne idan an auna shi da na’urar awon karfin bugun jini (wato spygmomanometer) wadda ta nuna awon jininsa ya kai, ko ya wuce, dari da arba’in bisa casa’in (wato > 140/90mmHg) kuma awon ya dauwama a haka. Sai dai wannan adadi da aka ambata yana sabawa saboda bambancin shekaru, jinsi (wato namiji ko mace), halin da mutum yake ciki, dasauransu.

A takaice dai, sai an je asibiti za’a iya tabbatarma mutum ko yana da cutar ko baya da ita.

MENENE YAKE KAWO CUTAR:

Ta la’akari da yadda wanna cuta ke faruwa ga mutane, an raba wannan cuta zuwa gida biyu. Kashi na farko - Sama da kashi casa’in (>90%) na mutane dake fama da wannan cuta, har yanzu ba’a san takamaiman dalilin da za’ace shi ya kawo masu wannan cuta ba sai dai akwai wasu abubuwa ko al’amura da aka alakanta ga faruwar wannan cuta ga wadannan mutane na kashin farko.

ALSO READ: Amfani 5  Da  Yayan Bagaruwa Da Ganyenta Keyi A Jikin Dan Adam

Wadannan abubuwan sun hada da yanayin kwayoyin halittar dan-adam, ma’ana ana iya gadon wannan cuta.

• Jinsin dan-adam (anfi samu a bakaken fata)
• Yawaita shan gishiri fiye da kima.
• Yawaita shan barasa (giya).
• Kibar jiki mai tsananin yawa.
• Rashin motsa jiki, da dai sauransu.

Kashi na biyu - A wannan bangare, an gano wasu cututtuka na musamman da suke kawo wannan cuta.

Cututtukan sun hada da:

• Cututtukan dake shafar kodar mutum.
• Cututtukan dake shafar kwakwalwa.
• Wasu daga cikin magunguna na bature.
• Wasu cututtuka dake shafar jijiyoyin jini, da dai
sauransu.

TAYAYA AKE GANE ALAMOMIN WANNAN CUTA:

Wasu daga cikin mutanen da suka kamu da
wannan cuta basu da wasu alamomi da suke ji, wasu kuma sukan ji kamar yawan ciwon
kai, fargabar zuciya, raguwar gani ko gani
dishi-dishi.

Wasu kuma suna zuwa asibiti ne da alamomi na illolin da cutar ta haifar musu (za’a yi bayani nan gaba). Wasu kuwa sai sunje asibiti dalilin wata
cutar, wurin bincike sai a gano cewa suna da
cutar hawan jini.

ALSO READ: Maganin Rage Kiba ko Tumbi Cikin Karamin Lokaci

Karin bayani a nan shine, ba wai ance da mutum yaji yana fama da daya ko wasu daga cikin alamomin can na sama kawai sai yace ya kamu da cutar ba. Wannan kuskure ne. Mutum ya bari sai yaje an auna shi domin a tabbatar masa ko yana da cutar ko bashi da ita, domin tabbatacciyar hanyar sanin mutum ya kamu da cutar hawan jini ita ce ta auna jinin da na’urar asibiti.

ILLOLIN CUTAR HAWAN JINI:

Wannan matsaloli zasu iya faruwa ga wanda bai dade da kamuwa da cutar hawan jini ba ko kuma ga wanda ya dade da ita sun kunshi.

• Ciwon koda wanda zai iya jawowa ta daina aiki.

• Raguwar gani ko makancewar ido.

• Ciwon shanyewar wani bangare na jiki kamar rabin jiki (wato Paralysis).

• Ciwon zuciya, da dai sauransu.
Sai dai abinda ya kamata a fahimta game da
wadannan matsaloli shine, ba cutar hawan jini kawai ke kawo suba.


Za’a iya samun su ta wasu cututtuka kamar ciwon suga (wato Diabetes Mellitus) da sauransu. Wadannan illoli sun fi faruwa ga mutanen da suke da wannan cutar kuma basa shan magani ko kuma basa sha kamar yadda likita ya umarta.

MAGANIN CUTAR HAWAN JINI:

Akwai magunguna kala-kala da ake bayarwa ga masu wannan cuta.
Suna yin amfani ne wajen tabbatar da daidaitar awon jini na mutum ta yadda ba zai yi yawa har ya kai ga samar da wadancan illoli da muka ambata ba Wadannan magunguna za’a same su idan anje asibiti wajen likita.

Haka kuma kula da wadannan abubuwa da zamu zana wadanda ke da alaka da wannan cuta suna taimakawa matuka wajen kiyaye kai daga samun wannan cuta ko rage matsalolinta ga wadanda suke da cutar,

ABUBUWAN SUNE:

• Barin shan barasa.
• Rage yawaita shan gishiri a abinci.
• Motsa jiki akai-akai.
•  Rage kiba mai tsanani, ta hanyar rage yawaita cin abinci fiye da kima, rage cin man kitse, motsa jiki da sauransu.
• Yawaita cin kayan lambu da ababen marmari kamar su lemo, yalo, karas, alaiyahu, zogale, rama, da danginsu.

Muna rokon Allah Ubangiji yakara mana lafiya.

Published on 2/may/2022 by: Abubakar D. Bature

1 Comments

Previous Post Next Post