Magana Jarice: Raina Kama Kaga Gayya Kashi Na Biyu 2

Magana Jarice: Raina Kama Kaga Gayya Kashi Na Biyu 2

 


Barkanku da sake kasancewa a wannan shafi namu mai albarka masu karatu in baku manta ba a wannan labari kashi na farko mun kwana ne Inda mai keken shanu yace da yautai, "Wanene dan uwanka da kake tsai dani dominsa?

To zamu dora,
Yanuna masa kare da ke barci,  yace Gashi Nan mai keke ya dubi kare yayi tsaki yace, Dama don saboda kare ka tsai dani? Karen me! 

Kai ar, Allah Wadaranka, sai ya kora shanunsa suka bi ta bisa Karen, Bai ko shura  ba, ya mutu hanji waje. Yautai ya tashi yabi shi yana kuka, yane cewa, Wayyo ni kaico na. Ka kashe min dan'uwa bai ci ma ba bai sha ma ba. nayi ma magana ka lura Ka ki don ka raina ni. To yadda kasa na zubad da hawayena yau,  kaima sai nasa ka zubad da naka. A bar ma batun hawaye, yadda kasa Dan'uwana ya bar duniya yau kaima kana barinta, In Allah yaso.

Mai keke yayi dariya yace Harkai nan dan tsuntsu Yadda kake zaka ce zaka iya sani kuka? Dubanni da kyau fa ka gani.
Yautai yace, to shikenan. Raina kama kaga gayya! Mai keken nan kuwa a gaba yake zaune,  buhunansa na baya.

RELATED: Magana Jarice: Raina Kama Kaga Gayya Kashi Na Farko 1


Da yautai yaga ya kora, sai yayai gaba kamar ya Wuce shi, sai ya dawo ya sauka bisa buhunan gero, mutumin nan bai sani ba. Yayi ta yi musu huda, gero na tsiyayewa, mutumin nan bai sani ba. In yaga kamar zai kamar zai waiwayo sai ya Boye tsakanin buhu. zuwa can gero ya tsiyaye, Sai yaji keke na kwaram-kwaram kamar ba kaya.

Ya tsai da shanu, ya sauka ya duba kaya yayi salati. Yautai ya tashi yace kadan ke nan,
Ai ban gaya maka ba, raina kama kaga gayya. Ya tashi ya sauka idon sa guda yayi ta tsatstsagewa sa, na tsalle mai keke ya ganshi
Ya dauki wani gatari nasa zai kwantara masa Sai ya tashi, ya sami kan sa. sa, ya fadi nan take Ya mimmike. Mai keke yace "Wash!" Yautai yace Tukuna Ai na gaya maka raina kama kaga gayya.

Mai keke ya ciji baki ya sauka ya daura wa daya san, keke ya hau ya kora ya nufi gida, yautai ya Komo ya sauka bisa idon dayan san, ya fara Tsatstsaga shi kuma yayi ta tsalle-tsalle yana harbe-harbe mai keke ya dube shi yace Lalataccen nan ya dawo.

ya dauki gatari ya tsaya tsai wai ya dube shi daidai ya sare sai ya tashi
Ya sami kan san. Sai ya fadi matacce. Ya sauka ya rasa abin da zai yi sai ya saba gatarinsa, ya nufi Gida yana cizon yatsa.

Yautai yace mutafi gidan ai na gaya maka raina Kama kaga gayya. da matarsa ta gan shi ya shigo Yana zage-zage sai tace masa, "Lafiya babba da Kai kana irin wannan mugun baki?"

Yace ina fa lafiya, wani dan tsuntsu duk yasa na kashe shanuna, wai don na taka wani kare a Hanya. 

Ya waiwaya sai ya ga yautai bisa tukwanansu, yace kin gan shi ma ya biyo ni,
lalatacce matarsa ta ce kai anyi katon banza
Yaya dan tsuntsu kamar wannan wanda baifi a Hadiye ba, zai ruda ka haka?

Sai ta fizgi gatari da fushi ta wurgi yautai dashi. Yautai ya tashi, ta sami tukwanensu duk suka fashe. Yautai ya koma cikin dakin matar ya sauka yace, Raina kama kaga gayya. Da matar ta waiwaya ta ganshi sai ta sake daukar Gatarin ta wurge shi da shi ta sami korenta, duk Suka fashe. 

Kai in gajarce maka labari dai sukayi
Tayin haka har ta fasa kaya dakinta duka. Yautai ya dube su, yace "Tukuna dai. "Raina kama Kaga gayya."




Daga nan mijin ya tuna da wata dabara, ya matsa Wurin matarsa , ya rada mata yace, rufe taga Maza, ni kuma in rufe kofa. mu rutsa shi mukama, Muyi masa irin kisan da muke so.suka zabura Gaba daya sukai waje suka rurrufe, suka koma Ciki. tarfa nan tarfa can, har suka kama shi a hannu, suka bude kofa da taga suka tsaya gardamar yadda zasu kasheshi, mijin yace,

Wura wuta zakiyi ki jefa shi. Matar tace a'a bahaka zamuyi ba, fige shi zakayi ni kuwa in nika Tattasai in tsoma shi a ciki, ko kuma ba haka zamuyi ba, in mun fige shi insa wuka in kwakule idanunsa yau, gobe in yanke kafa guda, jibi in yanke fiffike, mubi shi yanka gaba, gaba harya Mutu. Dan lalatacce,

Da yautai yaji haka sai yace, ta Allah ba takuba Raina kama kaga gayya.
Koda suka ji haka duk sai suka fusata, mai sai ta zaro wani takobin mai gidan dake nan tace, "Bari in sare shi" mijin yabar matar ta sare shi, Sai duka mai zai take shi, sai matar kuwa idonta Ya rufe don fushi, takai wa yautai sara dai, dai da Sa'adda mijin ke dukawa ya take shi, Sai ta sare kan mijin, ya fadi ya mutu. Yautai ya tashi ya fita yace, To Alhamdulillahi! dama hakin Da ka raina shi ke tsone ma ido.

Ganin wannan al'amarin yasa matar ya haukace Ta dauki gatari ta shiga daji, kowane tsuntsu tagani sai ta kai masa jifa tana cewa "Raina kama Kaga gayya".

To masu karatu anan muka kawo muku karshen wannan labari mai fadakarwa mai suna " Raina Kama kaga gayya" wanda yake cikin magana Jarice kashi na farko wanda Alhaji Abubakar Imam ya wallafa.


Written by: Abubakar D.Bature

Post a Comment

Previous Post Next Post