Wata rana yautai yana kiwo a bayan gari sai tarko ya kama shi. Yana nan yana kici-kici sai ga wani Tsohon kare ya zo. Da yautan nan ya gan shi sai Yace masa "Don Allah wannan kare ka dubi zumunci, kaji kaina kasake ni, kai kuma Allah ya
Taimake ka."
Kare ya tsaya kamar ya ki, ko kuma ya dan cinye Shi ne ya wuce yaga dai kamar ko yaci shi, bazai Kosar dashi ba.
Sai ya tafi kusa da shi, yasa baki ya tattaune tarkon nan, yautai ya kubuta.
Da yautai yaga an kubutad dashi sai yayiwa kare Godiya, ya tambaye shi inda za shi. Yace zashi naman abincine.
Shi kuwa kafin yazo nan a kama shi a tarko, ashe yaga inda wata 'yar akuya ta mutu, aka kai gindin Wata itaciya aka yar.
Saboda haka yace wa kare yazo ya kai shi, kafin Dare yayi kuraye su cinye. Ya tashi kare yana bin Inuwarsa har suka isa wurin. kare ya tsaya , yasa Hakori ya barke cikin akuya , yaci-yaci har ya koshi. Yautai yace masa, "Dayake ka koshi sai mu tafi kaga shekata , kullum in ka matsu da son
Abinci kazo ni kuwa in tashi in kewaya gari,
Inda naga wani abu da zaka iya ci inzo in kira ka Mu tafi."
RELATED: Magana Jarice: Raina Kama Kaga Gayya Kashi Na Biyu 2
Yace, to "Madalla! Mutafi in gani."
Da suka fara tafiya suka kai kan titi sai karen yace, Wallahi naman nan da naci ya kusa ya kware ni,
Da zaka dan dakatamin in kwanta nan in dan huta Kadan dana so.
Yautai yace, ai gaskiyarka kwanta ka huta in kana Son barci ma yi, ni kuwa zan hau nan in tsaya in Naga yara zan gaya maka katashi, don kada su Buge ka. Kare yace, to madalla!
Kwantawarsa keda wuya sai barci ya kama shi Can anjima kadan sai ga wani da keken shanu, Yana dauke da buhunan gero.
Da yautai ya hango shi sai yace masa, kai mai keke, kai mai keke, yi kwana don kada ka take Min dan uwa gashi nan yana barci.
Mai keke ya harare shi da fushi yace, wanene Dan uwan naka da kake tsai dani dominsa?.
To masu karatu anan muka kaho karshen
"Raina kama kaga gayya" kashi na farko
Ku biyo mu a kashi na biyu domin jin yadda zata kaya Tsakanin yautai da mai keken shanu.
Muna godiya da kasancewar ku a wannan,
Shafi na "Asua Daily Post" nine naku,
Abubakar D.Bature C.E.O na wannan shafi mai Albarka.
Mawallafin littafi: Alhaji Abubakar Imam.
Munji dadin wannan
ReplyDelete