ANNABI (S.A.W) YA FARA DACEWA:
Ya Ku Mutane Ku Bani Hankalinku, Domin Mai Yiwuwa Ba Zan Sake Kasancewa Da Ku Bayan Wannan Shekarar Ba, Saboda Haka Ku Saurari Abin da Nake Gaya Maku Da Kyau, Kuma Ku Isar Da Abin Da Zan Gaya Muku Ga Wadanda Basa Wannan Wuri a Yau.
Ya Ku Mutane Kamar Yadda Kuka Riki Wannan Wata na Hajji Da Wannan Rana ta Arafat Da kuma Wannan Gari na Makkah da Girma Kuma Abin Tsarewa, to haka Kuma Ku Rike rayukan musulmi da Kuma Dukiyoyinsu da Girma Abin Kuma Karewa.
Ku maida wa mutane Kayan Da Suka Baku amana, Kar Ku Cuci Kowa, Saboda Kar Wasu Su Cuce Ku, Ku tuna Fa, Hakika ALLAH zai yi Sakayya Akan Ayyukanku.
ALLAH (S.W.T) ya hana cin ribah (Wato Kudin Ruwa) Saboda Haka Duk Abin Da Aka Kulla ta Kudin Ruwa Sai a Warware Shi,
Kuyi Hattara Da Shaidan Domin Kiyaye Addininku, Yanzu Kam Ya Fidda ran batar da ku Akan Manyan Abubuwa (Na Sabo) Saboda haka Ku Guji Bin Shi Akan kananan ayyukan sabo.
Ya Ku Jama'a Hakika Kuna Da Hakki Bisa Matayenku, Amma Suma Suna Da Hakki Bisa Kanku, To Hakkin Su ne Akanku da Ku Ciyar Da Su, Kuma Ku Tufatar Da Su Akan Jin 'Kai, Ku Bi Da Su Kyakkyawan Biyarwa, Ku Kuma Tausasa Musu Domin Su Majibintan Al'amurranku Ne, Kuma Mataimakanku Ne, Hakki Ne Akansu Da Kar Su Yi Abota Da Duk Wanda Ba Kwa So, Kuma Su Nisanci Zina.
Ya Ku Jama'a Kuyi Kyakkyawan Bauta Ga
ALLAH (S.W.T) Ku Tsaida Salloli Biyar Na Farilla, Ku Azumci Watan Ramadan, Ku Kuma Bada Zakkah. Ku Aikata Aikin Hajji(In har kun samu damar yi).
Ku sani fa, kowanne musulmi dan'uwan
Musulmi ne, Dukkanku daya Kuke ba wanda
yake da fifiko Saman Wani Sai ta tsoron Allah, Da Aikata Kyawawan Ayyukka, ku tuna fa Wata Rana Za Ku Tsaya a Gaban Ubangijin ku Domin Sakamakon Ayyukanku, Saboda haka Ku yi hattara kada Ku yi Sake da hanya Madaidaiciya Bayan nawa fati.
Ya ku Jama'a ba wani Annabi ko manzo da
zai zo a Bayana, Kuma Babu Wani Addini da
zai zo a Bayan Addinin Musulunci , Saboda
Haka kuyi Tunani Sosai Akan Wannan Magana Dana Gaya Muku, Kuma Ku Fahimceta Sosai,
Zan Bar Muku Abubuwa Guda uku Ga Alqur'ani, da Ahalilbaiti, Ga Kuma Sunnah,Ta In Kun Bi Wannan Baza Ku Taba Bata Ba.
Allahu Akbar.
Allahu akbar
ReplyDelete