Gwamnatin Jihar Kano Karkashin Jagorancin Abdullahi Ganduje ta Amince da Sauya Sunan Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (KUST) da ke Wudil

Gwamnatin Jihar Kano Karkashin Jagorancin Abdullahi Ganduje ta Amince da Sauya Sunan Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano (KUST) da ke Wudil

 


Majalisar zartaswar jihar ta amince da hakan ne a zamanta na karshe da Gwamna Abdullahi Ganduje ya jagoranta.

Aminiya ta ruwaito cewa Aliko Dangote shi ne Shugaban Jami’ar, a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba, ya ce sauya sunan cibiyar ya biyo bayan shawarar da kwamitin ziyarar jami’ar ya bayar.

narwar ta kuma bayyana cewa an mika amincewar ga majalisar dokokin jihar domin nazarin dokokin da suka dace da suka kafa jami’ar domin yin gyara.

Sanarwar ta ce a yanzu za a kira KUST da sunan Aliko Dangote University of Science and Technology (ADUST), Wudil.

Wannan bashine na farko ba in kukayi la'akari da a baya ma gwamnatin jihar kano tayi irin wannan canji inda tamayar da jami'ar an mai suna (northwest University) zuwa (Maitama Sule University) muna fatan wannan canja suna yazama mafi alkairi ga wadannan jami'oi.

Post a Comment

Previous Post Next Post