Lamarin fashewar da ya afku a Kano ya baiwa 'yan Najeriya mamaki matuka da gaske. A baya dai gwamnati ta yi ikirarin cewa fashewar da ta afku ta iskar gas ce ba Bom ba, Sai dai shugaban makarantar da abin ya shafa ya musanta wadannan ikirari.
Ya tabbatar da cewa dan kunar bakin wake ne ya aikata hakan ba fashewar iskar gas ba.
• Yan bindiga sun kashe mutum 25 a karamar hukumar bukkuyyum dake jihar zamfara.
Shugaban makarantar yakara da cewa sun ga dan kunar bakin waken kafin tashin bam din.
Wadannan kalamai da suka fito daga bakin malami da daraktan makarantar za a iya aminta da su tare da tantance cewa su ne shaidun faruwar lamarin, rahotannin da ke yawo yanzu na cewa kimanin dalibai tara ne suka mutu sannan wasu dalibai da dama kuma sun jikkata.
Source: Jakadiyar Arewa
Reported by: Abubakar D. Bature