[BLOGGING]: YADDA ZAKA SAMU KUDI TA HANYAR BUDE BLOGGER WEBSITE A CIKIN SAUKI

[BLOGGING]: YADDA ZAKA SAMU KUDI TA HANYAR BUDE BLOGGER WEBSITE A CIKIN SAUKI



Assalamu alaikum yan uwa barkan ku da sake Kasancewa a wannan shafi mai albarka, Na "Asua Daily Post" darasin mu nayau akan blogger ne wato yanda zaku samu kudi a online ta hanyar mallakar website.

Kamar yadda a baya muja koyar da youtube tun daga farko har karshe, wanda shima kaface da ake samun makudan kudade, to ganin hakane yasa nace yakamata na kawo hanyar samun kudi ta blog domin wadanda suka kasa a harkar youtube saiku koma blog kokuma in mutum yana da lokaci yayi duka biyun.

To amma agaskiyar magana blog yafi youtube sauki, domin kuwa shi basa bukatar wani adadi na mabiya kokuma makallah wato masu kallo, su kawai abun da suke bukata shine ka tsara site dinka yayi kyau sannan kuma kana kawo lbr ko wani abun da kakeyi masu ma,ana, sai kuma ka sayi domain wanda shima baya wuce 1k to 3k zamuyi bayaninsa anan gaba, to idan ka cika wadannan ka,ida insha Allah saide kaji kudi suna sauka account dinka, domin kuwa suma ana samun kudade masu matukar yawa,

ALSO READ: Yadda Ake Bude Youtube Channel 2022

karamin albashi a wata shine $100 wanda a yanzu yake dai-dai da 56’000 to kunga ko iya 56k kake samu duk wata ai zaka rage zafi, ballema saika samu ninkinsa sau uku, a wata, ya danganta da yanda ka dage da aikinka, domin idan suka karbeka to zasu saka ma "ads" wato tallace-tallace tayanda masu ziyartar  site dinka suna karanta content dinka zasu dinga danna
Wannan tallan ta yadda samun zai karu sosai Sannan kusani harkar blogging bazata hana ka yin wasu al'amuranka na yau da kullum ba.

Shin Blogging Yana Bukatar Kashe Kudi?

Akwai Blogging na kyauta akwai kuma wanda sai mutum ya kashe kudi, sai dai wanda ya kashe kudi shine zai fi cin ribar dake cikin blogging.

Sannan akwai abubuwan da wanda ya biya kudi zai iya yi amman wanda bai biya ba ba zai iya yi ba.

Sannan misali wanda ya biya kuna samun mutane adadi daya to kudin da wanda ya biya zai samu to wanda bai biya zai samu rabinsa ne.

Menene Blog:

Blog daya ne daga cikin shafukan internet da ake sanya bayanai a yanar gizo, ta yadda idan ka shiga zaka ga bayanan da aka sanya akansa.

Dai-daikun mutane da kungiyoyi kan mallaki blog domin adana bayanansu a yanar gizo.

Yaushe Aka Fara Yin Blog A Duniya:

A karni na 9 aka fara harkar blogging a duniya inda mutane kan wallafa bayanan da ya shafi rayuwarsu akai, sai dai ana yinsa ne a salon kimiyar wancan karnin.

A shekarar 1999 aka kaddamar da shafin blogging mafi suna wato "Blogger.com"
mallakar kamfanin google.

A shekarar 2003 kuma aka kaddamar da WordPress shafin Blogging dake kan gaba a yanzu a duniya.

Abubuwan Da Yakamata Ka Sani Kafin Ka Fara Sana'ar Blogging:

Abinda zaka fara yi da farko shine Ka dauki bangaren da zaka maida hankali akai anan ana son ka dauki bangaren da zaka maida
hakali wajen yin rubutunka misali,  "asuadailypost.com" ta mayar da hankali akan harkar internet, computer da wayar hannu, Labarai da sauransu,  to kaima ka samu gabar da zaka maida hankali akanta wadda jama’a zasu sanka akanta.

ALSO READ: Yadda zaku hada Application a Wayarku Ta Android Cikin Sauki

Dolene ka fahimci shin wane irin mabiya ne da kai  Sannan ka tsara hanyoyin da zaka dinga amfani dashi wajen isar da sakonka, misali nace ina kawo labarin wasanni kuma sai naje nake tallatawa tsofaffi kaga a yankinmu babu abinda ya shafi tsofaffi da labarin wasanni don haka sai nayi amfani da shafukana na nemi matasa tunda abinda nakeyi sune suke da bukatarsa.

Ka dinga tsara bayanan ka da kuma lokaci kada kace kullum ka samu content to zaka dinga sakashi a wannan lokacin, a’a ka dinga tanadin kaya na yau da na gobe, ta yadda ba zaka sa mutane su gajiya da kai ba.

Ka dinga karanta rubutukan sauran marubuta ka dinga bibiyar masu yin rubuta mai alaka da abinda kakeyi.

Ka samar da tsayayyen salon rubutunka, kowa akwai irin salonsa kamar yadda in kana sauraron radio sosai to kana jiyo wani shiri zakace wannan tasha kazace to kaima ka kir-kiri salonka yadda duk wanda yaga rubutunka zai gane cewa wannan rubutunka ne.

Ka dinga kula sosai da kuskuren rubutu, matukar baka kiyaye wannan to zaka sanya jama’a su daina karanta rubutunka.

Ka tsara taken rubutu a takaice kuma mai
jan hankali masu karanta rubutunka.

Taken rubutu wato ( description) da shi ne ake jan hankalin jama’a a rubutu, yana da kyau blogger yayi nazari mai kyau tare da neman shawara wajen tsara taken rubutunsa, yana da kyau kafin ka saki rubutu ka sake duba rubutun.

Menene Banbancin Blog da Website:

Banbancin website da blog shine shi blog ko yaushe anaso da an shiga aga sabon abu yazana kana saka sababbin bayanai akai-akai.

Shi kuma website yawanci an gina shine akan wani bangare daban wanda in ka ga bayani akai, misali website na kungiyoyi ana tsara shine yadda idan ka shiga zaka ga bayanan kungiyar akai duk sanda mutum ya shiga wannan bayanan zai gani sai dai lokaci bayan lokaci ana iya yin
canje-canje.

A website din ma'ana yana saka bangaren blog inda za’a dinga samun sabbin bayanai shine akan website zaku ga an saka "blog post"

Waye Blogger?

Wanda ya mallaki blog kuma yake rubuce rubuce akansa shi ake kira da Blogger.
Idan kana da tambaya ko neman karin bayani akan wani abu muhadu a comment.


Nine naku Abubakar D. Bature C.E.O Na "Asua Daily Post"

3 Comments

  1. Dan Allah enaso inbude blog nawa ta wanne website zanyi amfani

    ReplyDelete
  2. Tayaya blog zasu fara biyana sune zasuce in bada account number ko ya zanyi pls na bude blog ne ina posting abubuwa masu amfani da suka shafi magungun musulunci da girkegirke

    ReplyDelete
Previous Post Next Post