Bismillahi, wassalatu wassalam'ala
Rasulullah, Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, yayi mana umarni da Shan Nonon Saniya domin akwai samun waraka acikinsa da yardar Allah. 'Yan uwa nasan bazai zamo abin mamaki ba idan mukace nonon saniya tanada matukar amfani ko kuma maganine mai matukar tasiri ga jikin dan Adam, abisa la'akari da sinadaran da nonon ya kunsa da kuma binciken da masana suka gudanar, daga cikin masana akwai fiyayyan halitta shugaban masana (s.a.w).
RELATED: Wasu Daga Cikin Amfani 1O Da Cin Naman Akuya Keyi A Jikin Dan Adam
Annabi s.a.w ya bayyana mana mahimmanci nonon saniya. Hadisi ya tabbata daga Abdullahi ibn mas'ud (R.T.A) yace manzon Allah (s.a.w) yace, kuyi magani da nonon saniya domin acikinta akwai waraka (sahihul jami'i 2929).
Haka har ila yau hadisi ya tabbata daga Imam Albagawi ya ruwaito daga mulaika bintu amru mazon Allah (s.a.w) yace nonon saniya warakane naman saniyar kuma maganine amma yawan cin namanta yanada illa, wato red meat.
KADAN DAGA CIKIN AMFANINSA
Nonon saniya yana maganin ciwon daji kuma yana kariya daga kamuwa da ciwon daji mussamman ga kasashen da suke da karanci hasken rana wato (Vitamin D). Shan nonon da zuma yana maganin gajiya da wasuwasi da yawan tunani (depression).
Shan nonon saniya Yana mganin kowace irin cuta saboda ita saniya tana cin kowana irin ice dakuma ganye, shan nonon saniya asamu zaitun sai azuba a cikin nonon saniya a juya shi sai adinga baiwa Mai sikila bi'izinillahi mai cutar zai sami lafiya.
Wallahu, A'alam
Written by: Salisu Muhammad