Amfanin Lemon Zaki Ga Lafiyar Dan Adam Da Kuma Sinadaren Dake Kunshe A Cikinsa

Amfanin Lemon Zaki Ga Lafiyar Dan Adam Da Kuma Sinadaren Dake Kunshe A Cikinsa

 



Lemon zaki dan ice ne mai dandanon zaki da tsami-tsami, mai nau'in kalolin jaja-jaja, ko ruwan daurawa:

Sannan kuma dan ice ne wanda ke cikin jerin Kayan marmari kuma yana dauke da sinadarai da magunguna, domin kuwa ruwan da lemon zaki ke dauke dashi yana maganin dattin ciki, da baiwa gabobi lafiya da kuma kara kwarin idanu idan an sha aka cinye har abin cikin yana sakar da ciki a fitar da kashi kan kari bada wuya ba!

Lemon zaki yana da sinadaran magunguna masu amfani da yawa a cikin sa, amma wadanda aka fi sani sune kamar haka:

• Vitamin A
• Vitamin C
• Beta carotene, Antioxidants
• Folate
• Thiamine
• Potassium
• Flavonoids,

Lemon zaki na taimakawa mutanen
Dake dauke da wasu daga cikin sanannun cututtuka kamar:

• Ciwon daji
• Hawan jini
• Cutar koda
• Cutukan zuciya
• Cutukan hanta
• Matsalar makoshi, makogwaro
• Kurarrajin harshe
•Matsalar narkewar abinci
• Kumburin ciki, dasauransu.

Domin sinadarin vitamin c da ke ciki na
saukaka zafin ciwo:

Vitamin A ya taimakawa ga karfafa karfin
gani, idan kuma sun hada karfi zasu taimaka
sosai da karfafa mazantaka da matantakar
dika jinsin biyu.

Yawan shan lemon zaki na saisaita hawan
jini, da nauyin jiki, yana rage kiba da kuma turo daskararren kashin da ke jimawa a ciki.

Yana kuma taimakawa wajen  wanko daskararren Kitsen dake dankare a jikin mutanen mu nayau da basa son motsi, basa son wahala, ga su da son a ci dadi duk kuwa yadda dadi zai haifar musu da matsala,

Wallahu a'alam


Written by: Abubakar D. Bature

Post a Comment

Previous Post Next Post