Amfanin Ganyen Tumfafiya Da Yadda Ake Magani Da Ita

Amfanin Ganyen Tumfafiya Da Yadda Ake Magani Da Ita


Ita dai bishiyar Tunfafiya, mutanen da suka gabata a shekarun baya su suka fi amfani da ita wajen maganin wasu cutuka dake damun su a wancen lokacin dasuka rayu.

Sai dai kuma a cikin wannan zamani da muke ciki mutane da yawa basu damu da ita bishiyar ba Kasan cewar É—aukar ta da mukayi cewa duk inda bishiyar Tunfafiya take to matattarar Aljanu ce a wurin, don haka ne ma ya sanya Bama kusantar ta musamman da tsakar rana ko da Daddare.

Abin da kuma wasu mutanen basu sani ba ita  wannan bishiya ta Tunfafiya tana da matuÆ™ar muhimmanci ga lafiyar mu kama tun daga ita centa, saiwar ta, ganyenta, fulawar jikinta, da kuma yayan ta.

• Amfani 5  Da  Yayan Bagaruwa Da Ganyenta Keyi A Jikin Dan Adam

•  Amfanin Rake Da Muhimmancinsa A Jikin Dan Adam

Insha Allahu a wannan bayani da zamuyi zamu kawo muku muhimmancin amfanin da wasu sassan jikin Bishiyar Tunfafiyakeyi a jikin dan adam.

GANYEN TUMFAFIYA:

shiwanna  ganyen yana maganin aljanu dakuma sammu wato sihiri,  ko asiri,  a wata hausar.

YADDA AKE AMFANI DA GANYEN:

dafarko za'asamu danyen ganyen tumfafiya a shan yashi ya bushe sai adakashi aturmi yadaku sosai sai a sami mara lafiya adinga shaka masa a hancin sa safe da yamma zai sami sauki da izinin Allah (S.W.A).

WANDA AKAIWA SAMMU:

shi za'asamu ganyen ne adinga zubashi a garwashi sai a rufe mara lafiyar kamar surace idan yashaki wannan hayakin to bi'izinillahi
Zai samu waraka.

Wallahu a'alam Allah yasa mudace.


Written by: Salisu Muhammad

1 Comments

Previous Post Next Post