[YOUTUBE]: Yadda Ake Bude Youtube Channel Harsu Fara Biyanka 2022 - Asua Daily Post

[YOUTUBE]: Yadda Ake Bude Youtube Channel Harsu Fara Biyanka 2022 - Asua Daily Post


 

Barka da zuwa shafin "Asua Daily Post"
A wannan lokacin zamuyi bayani akan
yadda ake bude YouTube channel Kuma a saitashi har YouTube su fara biyanka.

Kafin kace zaka bude YouTube channel
To dolene kana bukatar wadannan
Abubuwan kamar haka:
      

1. EMAIL ADDRESS

2. YOUTUBE APP

3. YOUTUBE STUDIO

Email address dinka shine YouTube Channel dinka.

Menene YouTube Channel:

YouTube Channel wani platform ne wanda yake mallakar kamfanin Google ne wanda idan harkana da Gmail Account zaka iya bude YouTube Channel dashi cikin sauki. Wanda idan har bayanka bude shi zasu baka damar kadinga saka videos ko kuma audio.

Bayan ka mallaki email address da 
YouTube App.

Zaka shiga cikin Youtube App dinka ka dora
Email din  bayan ka dora sai ka danna,
Create channel zai nuna ma blank space,
Sai ka zabi sunan da kake bukata ka bude
Youtube account dashi, wani lokacin kuma,
zaka shiga option inda aka rubuta EDIT CHANNEL bayan ka shiga zakaga sunan
Email dinka sai ka goge sunan ka saka
sunan da kakeso channel dinka ta kasance,
haka ake bude YouTube Channel.

YOUTUBE STUDIO:

Ana amfani dashi gurin ganin Rank na channel dinka, yin Edit,  kamar dora Thumbnails,
Listed and unlisted a takaice.

YADDA ZAKA SAITA CHANNEL DINKA:

Abu nagaba shine idan ka taba profile
wasu Zane ko digo guda uku asama ta
gefen dama.

naka zai nunamaka wasu rubutun sai kazabi YouTube studio, daganan zai budemaka,
A gefen hagu zakaga wasu rubutun to
a wajen zakaga alamar Dala($) sai kataba.

Idan yabude zakaga wani flower da kamar hoto sannan akasan shi akwai wani rubutu,
idan kana Niger ko Afghanistan ne to ba
za'a baka daman yin rigister domin
Baza abiya kaba sai dai Idan zaka
canza location.

Idan kuma kana Nigeria ne to shikenan
zakayi babu matsala.

Yadda zaka canza location din shine zakayi zooming na wannan flower dake da wasu rubutun akasa acikin rubutun zakaga inda aka rubuta "Update location" sai ka taba,
idan yabude zakaga channel sai kataba,
bayan nan zakaga setting sai kataba,
sannan kajawoshi kasa zakaga advance
channel setting sai ka taba,

Idan yabude sai kazabi always ko only,  sannan kayi zooming sai ka canza location din, zakaga keyword sai kasaka sunan abinda kakeso ka koyar a channel naka din, sai kajashi kasa, 

zakaga save sai ka danna sannan kayi sama ta gefen dama zakaga return to sai ka
taba zai maidoka can inda zakaga
An baka daman saita komai.

Sai ka Kara taba digon nan guda uku asama wadanda suke gefen dama idan kataba zai nuna maka sai kataba desktop,

Idan yabude ta gefen hagu zakaga wasu
rubutun sai ka taba alamar Dala($)
zai kaika can wurin na farko da kataba,
A wurin zakaga an rubuta maka cewa zaka
Sami subscribers 1,000 da watch time our 4,000 A cikin shekara guda sannan ne zasu fara biyanka na duk wani video da kasaka sai kataba wannan alama dake wajen mai kalar blue sannan sai kaja page din kasa,

To akasan ta gefen dama zakaga wasu rubutun guda biyu ko uku, zakaga setting sai ka danna Idan yabude zai kaika inda zaka canza location dinka awajen zakaga, 

"Future eligibility" sai kataba, zai bude to akasa, zakaga "Status and the Future" sai kataba, sai kayi zooming zakaga logo na channel naka zakaga Verify sai kataba, zai nuna maka inda zaka saka phone number ka sannan za'a tambayeka ta wace number kakeson su turamaka verification code sai kataba send me verification code, idan kasaka number sai kataba submit sai ka jira
A turamaka code din sai kasaka, kayi submit zakaga sunyi verified naka shikenan.

Amma Kada ku manta idan kuna saka, 
video da ba naku ba YouTube zaau
kulle maka account sabida haka akiyaye
Kusan yadda za'ayi ku kirkiri video naku na kanku ku saka,

HANYOYIN SAMUN SUBSCRIBERS 1,000
DA  WATCH TIME HOURS 4,000

1. Zakayi tunani da nazari akan bidiyon da
zakayi watau kayi bidiyon da mutane
suke so domin shi zaikara sa mutane su so channel dinka.

2. Kasami camera mai haske Kuma ka koyi yadda akeyin Editing domin gyara bidiyon ka.

3. Kayi videos guda biyu akalla duk sati,
Kuma bidiyon ka yazamo mai tsawo ne.

4. Ka bude group a WhatsApp da Telegram sannan ka mallaki page a Facebook, sannan kayi share na link din groups naka a Facebook domin ka mallaki jama'a domin idan kayi video kayimusu share a groups din.

5. Ka tanadi 'yan kudade kadan sannan
kanemi sanannun masu YouTube channel wadanda ka yadda da su ka biyasu suyi maka tallan channel naka suyi share wa mutane akalla sau biyar zuwa sau goma.

Idan har kayi haka to insha Allah acikin
watanni biyu zaka Sami 1,000 subscribers da 4,000 watch time hours,

sannan channel dinka zai zamo sanan nen channel aduniyar internet sannan YouTube, 
zasu dinga biyanka ya danganta da kokarinka.


Written by: Abubakar D. Bature

2 Comments

Previous Post Next Post