Yadda Zaka Kare Facebook Dinka Daga Masu Hacking

Yadda Zaka Kare Facebook Dinka Daga Masu Hacking

 


Barka da zuwa shafin "Asua Daily Post"  a kullum ana kara samun rahotannin yadda masu kutse ke ci gaba da kwakwkwace asusun mutane  da dama daga masu amfani da dandalin sada zumunta na Facebook.

Sai dai hakan na da alaÆ™a da sakacin da mafi yawa ke yi game da daukar matakan kariya, a wannan rubutu na yau, zamu kawo wasu daga hanyoyin da mutum zai bi domin bai wa asusunsa kariya ta musamman daga  madatsan.

Yana da kyau ka dinga canja “Password” dinka akalla bayan sati daya zuwa sati biyu.
SharuÉ—an sauya password.

A guji sanya lambobi 123456 ko sunanka, ko kuma lambar wayarka ko sunan budurwarka, ko unguwarku,  ka sanya harufa da kuma lambobi, kai har ma da symbols kamar #!@*? da dai
Sauran su.

Sannan kada ka yarda ka sanar da wani wannan password din naka.

A kula kada kayi amfani da password guda ɗaya a dukkan abubuwanka misali Password a Email da kuma Facebook da sauran abin da kake buɗewa duk su zama iri ɗaya, yin hakan ganganci ne da zai buɗe ƙofa ga masu kutse.

Sanya karin Email a kan account dinka: A kalla ina bada shawarar kayi adding Email kamar guda 3 a kan account dinka, ka ga kana da cikakken iko akan asusun ta yadda duk wani motsi ko wani yunjuri da aka yi kai tsaye zaka samu bayani.
Ka rufe emails din ta yadda ba wanda zai iya gani.

A settings na Email din ka mayar da shi babu wanda zai iya ganin su sai kai kadai wato “only me” a yaren Facebook kenan.

Sannan lambar wayarka ta zamo tana aiki kana samun sakonni a cikinta, da yawa lambobin da muka bude Facebook muna rasa layukan, amman har yanzu mun gaza cire lambar daga kan
Facebook din.

Rashin sauya wannan lamba shi ma na taka rawa wajen haddasa  rasa asusun mu na Facebook.

Ka kunna “Login Approval” da “Two-Step Verification.

Wannan zai baka damar jin duk wani motsi na account dinka, sannan idan zaka yi login, dole sai an turo maka da code ko kuma kayi approving ta wayarka, sannan a nan bangaren zaka iya samar da “code generator” ta yadda zaka samar da wani code wanda kai kadai ne ka sanshi, idan ka zo yin login bayan password to shi ma zaka saka shi.

Ka dinga yin log out duk sanda zaka sauka.
Ka guji yin saving din bayanan account dinka a waya ko Computer din da ba taka ba. Ka tantance Link ko Application kafin bashi damar amfani da Facebook dinka

Sau da dama idan kana amfani da manhajoji ko wasu shafukan intanet su kan baka zabi na ka yi amfani da Facebook domin yin rajista da su, shi ne zaka ga an rubuta maka “Continue with Facebook” ka tabbatar da ingancin ko wane daga ciki kafin ka amince, domin gudun faÉ—awa tarkon yan hacking.

Hackers na yin amfani da link misali. www.share.facebook.com wato yin subdomain kenan, a ƙirƙiri wani adireshi na bogi, domin satar bayanai, ya zama dole ka lura da links da ake aika maka, shin Facebook.com ne kai tsaye ko akasin haka.

Ka dinga updating din browser ko application dinka lokaci zuwa lokaci. Ka daina yawan tura Friend Request ko yawan yin Accept, ka kula sosai wajen karbar wanda baka san shi ba, yana da kyau ka duba Profile É—in mutum kafin ka karÉ“e shi. Ka daina yawan yin sharing na wani link da baka tantance shi ba, Muna ganin inka kiyaye waddan nan ka'idojin zaka kubuta daga sharrin hack

1 Comments

Previous Post Next Post