Wani lokaci ana samun wannan matsalar, sai kayi tafiya mai nisa zuwa ATM MACHINE domin in zaka cire kudi sai ka nemi ATM ka rasa, ma'ana ka manta da shi a gida.
Idan kabi wannan process zaka cire kudinka ba tare da ATM CARD amma idan kana tare da wayar da kake jin Alert lokacin.
Zan kawo na kowanne banki daya bayan daya.
1. FIDELITY BANK
* 770*8* AMOUNT# da layin da kayi register fa bawai da wani ba,domin idan bada Sim din bane bazaiyi ba.
Zasu baka dama ka zabi one time pin wato OTP sai kasa sannan pin din bank din domin kayi wannan transaction din.
Dan haka code din da suka tura maka dashi za kayi amfani, Dan haka sai kaje kan ATM Machine ka danna kowacce number ne saika zabi paycode cash out ko kuma ka danna 4cash.
Sannan saika danna wannan pin din na OTP da suka tura maka saika sanya adadin kudin kamar yadda muka koyar a baya, shikenan zasu turo maka da kudinka.
2. UNION BANK
Kawai ka danna * 826 # sai kai generating na paycode tare da pin sai kabi hanyar da muka nuna a baya saika sanya pin din akan machine din sannan ka zabi paycode sannan kabi hanyar ta karshe wanda zasu rubuta maka shikenan saika cire kudinka.
3. UBA
Zakayi amfani da layin da yayi register dashi a Bank din naka wato wanda ka bude account din dashi sannan saika danna* 919* 30 *amount #.
zasu tura maka gurin da zaka zabi pin din sannan da inda zaka sanya paycode dinka zasu tura maka code na cash out ta layin wayarka kai tsaye saika je kan ATM Machine din ka zabi paycode cash out, saika sanya cash out code dinka saika sanya adadin kudin da kake bukata sannan ka danna Ok
bayan sun tabbatar da transaction dinka yayi verified to zasu tura maka kudinka.
Written by: Salisu Muhammad
Kuci gaba da kasance wa a wannan shafi mai albarka na "Asua Daily Post" domin Samun abubuwan da zaku dinga karuwa da su.
Mun gode.
Zamu gwada
ReplyDelete