YADDA KANKANA TAKE AMFANI A JIKIN DAN ADAM

YADDA KANKANA TAKE AMFANI A JIKIN DAN ADAM


   

Kankana nada amfani sosai a jikin dan Adam musan man ma a lokacin da ta nuna sosai don masana sun ce sinadaran nunannar ya fi taruwa sosai musamman beta-carotene dake cunkushe a cikin jan tozon nan wanda ke matukar taimaka wa idanu.

Kankana tana da matukar mahimmaci kuma sananniya ce a cikin ‘ya’yan itatuwa, wadda yayanta ke dauke da sinadarai masu gina jikin dan adam, kamar su vitamin B, niacin, folate da kuma irinsu magnesium, potassium, manganese, iron, zinc, phosphorus, copper, etc.

WASU DAGA CIKIN AMFANIN KANKANA A JIKIN DAN ADAM.

Sinadarin vitamin C dinta na taimako wajen maganin cututtuka da dama.

Nitric oxide da wasu sinadaren kankana na taimakon masu ciwon zuciya da hawan jini.

Sinadarin arginine dake cikinta na kara yawan nitric oxide dake kara ma namiji karfin gaba.

Tana maganin ciwon daji kala-kala, da kuma ciwon koda.

Yayan kankana suna samar da sinadarin multivitamin B, wanda yana karawa jikin dan adam lafiyar jini.

Tana da sinadarai masu kara karfin kashi  bone  da kuma maganin kumburin jiki musamman gabban jiki (joints).

Zakin cikinta kuma na bawa mutum karfi, tana kuma kara wa jiki ruwa.

Yayan kankana ana amfani dasu wurin magance ciwon diabetes, idan aka tafasa ruwa yayan kankana 1-litre na tsawon mintina 45, sai a ringa shan ruwan kamar shayi.

Yayan kankana suna taimakawa wurin samun karfin jiki bayan rashin lafiya sannan kuma suna kara kaifin tinani.

Yayan kankana suna da sinadarin lycopene wanda keda kyau ga fuskar dan adam da kuma kara lafiyar namiji.

Tana haifar da samuwar wadataccen barci,
kankana na taimaka wa fata saboda sinadarin lycopene dinta.

1 Comments

Previous Post Next Post