Yadda Ake Sallar Gawa a Musulunci

Yadda Ake Sallar Gawa a Musulunci

 


Malamai na Mazahabobi sunyi ittifaki akan cewa  (SALLAR JANAZAH) farillah ce ta kifaya,  wato irin farillar nan wacce wani zai iya dauke wa wani.

Sai dai an ruwaito daga Asbag daya daga almajiran Imamu Malik (R.A).
cewar Shi Sunnah ce awajensa.

Za’a iya yin Sallar gawa akowanne Lokaci ko dare ko rana, Inji Iman shafi'i (R.A).

Amma Imam Ahmad da Imam Abu Haneefa (R.A) Sunce Makruhi ne ayi sallar Janazah alokutan nan guda Uku.

1. bayan Sallar asubah har zuwa fitowar rana.

2. Bayan sallar la’asar har zuwa faduwar rana.

3. Lokacin da Limamin Jumu’a ya hau kan mimbari yake khudubah.

Shi kuwa Imam Malik (R.A) Yace za'a iya yin Sallar Janazah a kowanne lokaci in banda lokacin fitowar rana da kuma lokacin faduwarta yace Makruhi ne.

SHARUDANTA:

Dukkan Maluman Mazhabobin sunyi ittifaqi akan cewa wadannan sune sharudan ingancin Sallar Janazah:

1. Tsarki da alwala.
2. Suturce Al'aurah.
3. Kallon Alqiblah.

Amma Sha’abi da Ibnu Jareer sunce za’a iya yi ko ba tare da alwala ba.

Imam Shafi'i da Abu Yusuf sunce Limami yana tsayawa ne adaidai kan mutum Namiji, ita kuma mace Liman zai tsaya ne adaidai tsakiyar ta.

Amma Imam Malik da Imama Abu haneefah Sunce Liman zai tsaya ne adaidai kirjin Namiji, ita kuma mace zai tsaya ne adaidai tsakiyarta.

KABBARORINTA:

Kabbarori hudu ake yi asallar janazah abisa ittifakin Mazhabobin nan hudu sai dai an ruwaito Kabbara uku daga Imam Ibnu Sireen.

Sannan akwai wata ruwayar daga Abdullahi dan mas’ud (R.A) yace:

Manzon Allah (S.A.W) yayi kabbara 9 abisa Janazah, Sannan yayi 7,  Sannan yayi 5, Sannan yayi 4. Kuyi ta kabbarawa mutukar Limaminku ya kabbara.

Koda ya kara abisa hudu to sallar ba ta baci ba, Imamush-Shafi'i yace zaka daga hannuwanka zuwa kafadunka ayayin dukkan kabbarorin.

Amma Imam Malik da Iman Abu haneefah
sunce ba zaka daga hannuwanka ba sai dai
a kabbarar farko kawai.

Karanta Fatiha bayan kabbarar farko, Farilla ne awajen Imam Shafi'i da Imamu Ahmad.
Amma Imamu Malik da Abu Haneefa Sunce,

Ba zaka karanta komai ba daga cikin ayoyin
Alkur'ani Sannan ana yin Salatun Nabiyyi (S.A.W) sannan kuma sai Addu'a ga mamacin da sauran al'ummar musulmi a bayan Kabbara ta biyu data uku da ta hudu ajere.

Sannan mutum zai yi sallama ne guda biyu abisa Mazhabobi uku.

Amma Hanbaliyya sunce Sallama daya zaka yi a damanka.

Aduba Thamrud-dany Babin Sallar Janaza da kuma Rahmatul-Ummah shafi na 81.


WALLAHU A’ALAM.

Allah ya yasa mu cika da imani.

2 Comments

Previous Post Next Post