Munanan illolin da shan taba sigari yake haddasawa ga lafiyar dan adam

Munanan illolin da shan taba sigari yake haddasawa ga lafiyar dan adam

 



Taba wadda akafi sani da "sigari" na daya daga Cikin abubuwan sha ta nau’in hayaki wadda take dauke Cikin  makunshin takarda.

Taba dai nau’ine na ganye wadda ake nomawa ana busarwa, 
Ana kuma siyarwa da manyan kamfanoni domin su sarrafata a makunshin takarda sannan su siyar. 

Wasu na Shan taba cigari ne domin nishadi,
wasu kuma domin burgewa a yayin kuruciya. Wasu kuma domin burgewa dasauran mabanbantan ra’ayi.   

Sinadaran da ta Taba ta kunsa sun hada da nicotine, Ammonia, methylamine, Arsenic
carbon monoxide etc.

Sannan Taba sigari tana dauke da sinadarai Sama da guda 600 idan an konata tanasamar da chemicals guda 7000, wanda akalla
Chemical 70 nada alaka da cutar Sankarau wato Cancer.

Hatsarin Taba sigari ga jikin dan Adam
Taba nada hatsari kwarai da gaske misali:

1.Taba na haifar da cutar Sankarar Baki

2. Taba na haifar da cutar tarin fuka da tarin shika.

3. Taba nasa cutar rashin gani

4. Taba nasa cutar rashin ji na kunne da sauran cutttukan kunne

5. Taba nasawa mutum  ciwon zuciya, ciwon hawan jini

6. Taba nasa ciwon Sankarau.

7. Taba nasawa mutun ya rasu da kuruciya.

Sabo da Haka Jama’a yakamata a daina shanta gaba daya ko kuma a  rage shan Taba sigarin domin lafiyar mu.


Rigakafi yafi magani.

Allah yasa za'a kiyaye.

1 Comments

Previous Post Next Post