Kamar yadda mutum kan ji zafi ya nemi ruwa mai sanyi ko kuma ya nemi wuri mai iska ya kwanta a wannan lokaci na zafi haka wasu dabbobi da kwari kamar su karnuka, kunami da sauransu.
Wasu masana kiwon lafiya sun bayyana cewa a wannan lokaci na zafi mutane sun fi kamuwa da cutuka kamar zazzabin cizon sauro, saran maciji, kunama da kuma cizon kare dasauran su.
Masanan sun ce ya kamata duk lokacin da aka shiga yanayi na zafi a wayar wa mutane kai na yadda zasu kiyaye kansu daga kamuwa da irin wadannan cutuka kamar haka:
1. A tabbatar an duba rassan itatuwa da kuma tarin ganye dake karkashin itatuwan da suke domin macizai za su iya zama a irin wadannan wurare.
2. A daina barin tagogi da kofofi a bude ba tare da A na kula da duk wani mosti ba, za a iya saka murfin kofa mai raga, kafin ainihin kofar shiga saboda kiyaye wa.
3. A tabbatar ana tsaftace muhalli ana rufe kayan abince don gujewa shigowar tsaka.
4. A yi amfani da maganin sauro domin gujewa kamuwa da Zazzabin Cizon Sauro.
5. A yawaita shan ruwa.
6. A kula da tsaftace yara.
7. A guji Watsa Ruwan Sanyi A Kai Domin Samun Saukin "AZUMI" domin Sanyi Yana shigar maka kai yau da gobe watarana zai tambayeka.
Allah ya kare mana lafiyar mu Amin.
Written by: Salisu Muhammad
We are highly thanks for being with this blessed site "Asua Daily Post"
Zamu kiyaye
ReplyDelete