Har kullum ma'abota kallon wannan shiri mai farin Jini suna ganin yadda take kayawa a Gidan badamasi inda in baku manta ba a satin da ya wuce aka nuna cewa Alhaji badamasi ya mutu,
Bayan cimma matsaya akan zai bawa kowane daya daga cikin "ya yan nasa naira na gugar naira har naira milliyan goma ga kowane dayansu.
ALSO WATCH FULL VIDEO 👇
Mutuwar tasa ta janyo cece kuce a tsakanin ma'abota kallon wannan shiri inda wadansu suke cewa,
Indai har da gaske Alhaji Badamasin ya mutu tofa Suna ganin sunyi hannun riga da wannan shiri.
To fa tirkashi! Masoya wannan shiri kusha kuriminku a wannan sati ta sauya zani.
Bayan tirka - tirkar da aka sha da kuma rigin gimu da "ya yan Alhajin keyi akan rabon gadon wanda yaya dan kwambo ke jagonta,
To bayan yaya dan kwambo yasa sauran
"yan uwansa sunyi wa mutumin da yace yana Bin mahaifin nasu bashi harna naira biliyan Biyu Bore.
Hartakai sun kora shi waje inda suka bar taska a shaye daga shi sai gawar Alhaji badamasi.
Inda afkuwar hakan keda wuya garin gane - ganen malam taska ya gano kafar Alhaji badamasi na motsi a cikin makara.
Ma'ana dai kusha kurimin ku ma a bota kallon wannan shiri mai sa nishadi Alhaji Badamasi dai bai mutuba.
Kubiyo mu a "GIDAN BADAMASI SEASON 4 EPISODE 14" Domin kallon yadda zata kaya.
Kuci gaba da kasance wa a wannan shafi mai albarka na "Asua Daily Post" domin kasan cewa a cikin nishadi a koda yaushe.
Written by: Abubakar D Bature.