AMFANI 12 DA GWAZA KO MAKANI DA GANYENSA KEYI A JIKIN DAN ADAM

AMFANI 12 DA GWAZA KO MAKANI DA GANYENSA KEYI A JIKIN DAN ADAM


1. Ganyen gwaza na dauke da sinadarin
VitaminC, wanda ke kare mutum daga kamuwa da cututtuka.

2. Yana kare mutum daga kamuwa da cutar daji ta kowace iri.

3. Yana ragewa da kare mutum daga kamuwa da cutar siga "Diabetes"

4. Ganyen makani wato gwaza na dauke da sinadarin "VitaminA, wanda ke kara karfin ido sannan da kare ido daga kamuwa da cututtuka kamar su yanar ido,amosanin ido, makanta da sauran su.

4. Yana taimakawa wajen nika abinci, kawar da ciwon ciki sannan da hana yawan yin bahaya.

6. Yana hana fatar mutum tsufa da sauri sannan da kawar da cututtukan dake kama fata.

7. Yana ƙara ƙarfin jijiyoyin jiki.

8. Ganyen gwaza na kere mutum daga kamuwa da hawan jini.

9. Yana dauke da sinadarin "Calcium" wanda ke kara karfin ƙashi.

10. Ganyen gwaza na dauke da sinadarin
Folate, wanda ke inganta girman dan dake ciki sannan da hana mace mai ciki kamuwa da hawan jini.

11. Yana kara jini a jiki musamman ga yara kananan.

12. Yana Kara kaifin kwakwalwar mutum musamman wajen hana mantuwa.


Written by: Abubakar D bature

1 Comments

Previous Post Next Post