Wasu Daga Cikin Alamomin Da Ake Gane Daren Lailatul Kadari

Wasu Daga Cikin Alamomin Da Ake Gane Daren Lailatul Kadari


 


Daren lailatul kadari yana da alamomi da ake gane shi da su, wadannan alamomi suna kasancewa ne a cikin daren karan-kansa:

1. Dare ne mai haske, babu zafi ko sanyi
A cikin sa.

An karbo daga Jabir Dan Abdullahi (Radhiyallahu Anhu) ya ce:

Hakika ni an nuna mini daren lailatul kadari, sannan an mantar da ni shi yana goman karshe na Ramadan, dare ne da babu sanyi ko zafi a cikin sa, kuma mai haske ne, Ibn Khuzaima.

2. Rana tana fitowa da safiyar daren fara tas,  Lokacin da aka tambayi Ubayyu
Dan Ka’ab (R.T.A) a kan alamomin daren lailatul kadari, sai ya ce:

Alamar da Manzon Allah (S.A.W) ya ba mu labari ita ce, rana tana bullowa a wannan rana babu haske a tare da ita,  "Tirmizi".

3. Yanayi zai canza ya zama mai dadi, za a ji iska mai dadi, Ibn Khuzaima da Dayalisi.

4. Samun natsuwar zuciya da kimtsuwa, da kuma farin ciki da samun jin dadin ibada.

5. Za ka iya ganin shi "lailatul kadari" a mafarki, kamar yadda sahabbai suka gani.
Za'a iya yin mafarkin ga shi ana ibada a cikin daren.

6. Rana za ta fito babu zafi "idan lokacin zafi ne"

Wadannan su ne alamomin da ake gane daren lailatul kadari.

Amma cewar da ake itatuwa za su fadi su yi sujuda, rana za ta kusanto (kasa-kasa), taurari za su kusanto (kasa-kasa), karnuka za su daina kuka, wannan tatsuniya ce aka kaga a cikin addini, wanda kuma ba gaskiya ba ne.


Allah ya datar da mu da wannan garabasa.

Amin.

1 Comments

Previous Post Next Post