Shahararren dan gwagwar mayar siyasa shugan kungiyar Arewa Media Abudulmajid Danbilki Commander yayi wani furuci bayan fitowarsa daga gidan gyaran hali.
Inda yake cewa zuwansa kurkukun samun babbar nasara ce a gareshi yaji dadi kuma
Ya godewa Allah da ya kaddara zuwansa kurkukun domin a cewar sa ya kubutar da mutane da dama.
Wasu ya biya musu tara wasu ya daukar musu lawyer saboda basu da lawyer. Sannan kuma yasa an saka security light guda 40 Domin samar da cikakken tsaro a gidan gyaran halin.
gyaran halin ya zame musu gobarar titi yace ya tarar suna fama da matsanan cin rashin ruwan inda baiyi wata-wata ba yasa aka fara haka musu bowl-bowl. Saboda haka ne yake cewa shi zuwansa kurkuku ya zame masa babban alkhairi.
Tags:
News