Anan zamu iya cewa menene dalilin da ya haddasa yaki tsakanin makwaftan kasashen gudu biyu.
Batu dayane wato shiga kungiyar (NATO)
Ko kun san cewa Russia da Ukraine sun taba
Zama a matsayin kasa daya a karkashin
Tarayyyar (SOVIET).
Russia kasar da tafi karfi a cikin kasashe goma sha biyar da suke cikin tarayyar soviet.
Ukraine kuma itace kasa ta biyu mafi karfi a cikin tarayyar a lokacin.
Ukraine tana cibiyoyin tsaro da dama dakuma kasar noma mai fadi kuma itace take a jiye da makaman nuclear tarayyar Soviet.
ALSO WATCH FULL VIDEO 👇
RELATED POST: Rikicin russia da da ukraine yana dada tsamari yayin da nigeria zata fara jigilar dawo da yan kasar ta a ranar laraba.
Tarayyar Soviet ta rushe ne a shekarar 1991.
Kuma a shekarar ne Russia da Ukraine kowaccen su ta samu yancin kanta.
Ukraine taci gadon mafi yawancin makaman nuclear tarayyar Soviet.
Amma a shekarar 1994 ta mikasu ga kasar Russia.
Ita kuma kuma gwamnatin Russia tace zata dinga bawa kasar ukraine tsaro.
Inda tayi alkawarin mutunta kasar ukraine a matsayinta ta kasa mai cin gashin kanta.