Rundunar yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wata tsohuwa da ake zargin ta saka wani matashi mai shekara 17 ya kwakulewa wani yaro mai suna mustapha Dahiru ido don a hada musu layar zana.
Rundunar yan sanda ta ce ta kamo matar ne bayan koke da suka samu daga jama'ar unguwa da yan sa kai na yankin unguwar Dan Tsinke a karamar hukumar Tarauni a kano.
Tun kafin yan sanda su kai ga kamo matar da ake zargi da sa matashin ya cirewa yaron ido, kungiyar tsaro ta 'yan sa-kai ta Dan Tsinke da ke kusa da Unguwar Sheka suka kamo matashin da ake zargi da cirewa yaron ido dan shekaru 10-11.
Matashin da ake zargi ya shaida musu cewar wata tsohuwa ce ta umarci da ya kawo mata ido don ta hada masa layar zana, kamar yadda Rabi'u Suleiman Mai Matasa mataimakin sakatare na kungiyar 'yan-sa kai ta Dan Tsinke a kano ya ce.
SP Abdullahi Kiyawa kakakin rundunar yan sandan jihar kano ya tabbatar da faruwar al'amarin, ya kuma ja hankulan al'umma da su ringa sanya ido kan abubuwan da ke faruwa a kewayen su, don kaucewa afkuwar irin wannan lamari.
Ko a makon da ya gabata sai da aka sami wani matashi da ya tura 'yar uwarsa a cikin rijiya, a yankin karamar hukumar Rimin Gado a Kano, tare da wani matashi da ya kashe wata yarinya, yar makwabcin gidansu, bayan da ya nemi kudin fansa daga bisani bai samu ba saiya kasheta.